A wata hira da ta yi da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ɗahira Da’awi ta bayyana cewa nazarin rayuwar Sayyida Fatima Zahra (S) ta fuskar tarihi da aƙida yana nuna cewa ba wai abin koyi ce kawai a cikin iyali ba, a’a, ta kasance mai taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da al’amuran zamantakewa, siyasa da gina wayewar al’umma.
Da take magana kan matsayin mace a cikin Alƙur’ani, ta ce aya ta 71 a Suratut Taubah ta bayyana matsayin mace a cikin al’umma, inda Allah Ta’ala yake cewa:
«وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِیَاءُ بَعْضٍ ۚ یَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَیَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنکَرِ وَیُقِیمُونَ الصَّلَاةَ وَیُؤْتُونَ الزَّکَاةَ وَیُطِیعُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ…»
“Kuma muminai maza da muminai mata, sassan su masu taimakon (kuma abokan) sassan su ne; suna umurni da alheri, kuma suna hana abin da ba daidai ba (mummuna), kuma suna tsayar da salla, kuma suna bayar da zakkah, kuma suna biyayya ga Allah da Manzon Sa…”
Ta bayyana cewa wannan aya tana tabbatar da cewa maza da mata muminai suna da alhakin taimaka wa juna da kula da al’amuran al’umma, ciki har da umarni da kyakkyawan aiki, hani da mummunan aiki da kuma tabbatar da koyarwar Allah.
Mai fafutukar al’adu ta bayyana cewa Sayyida Fatima (SA) ita ce cikakkiyar misali ta aikata wannan koyarwa. Ta ce rayuwarta ta nuna cewa kasancewar mace a cikin al’umma bisa koyarwar Musulunci, kasancewa ce mai cike da nauyi da mutunci; ba wai zama a gida tare da ware kai daga al’umma ba, har ta hana al’umma amfana da basira da ƙwarewar mata, haka kuma ba wai mayar da mace abin nunawa ko kayan amfani ba ne.
Ta ƙara da cewa Sayyida Fatima (SA) ta kasance ginshiƙin soyayya, tausayi da tarbiyya a cikin gidanta, amma idan bukata ta taso, tana fitowa cikin al’umma cikin mutunci da kiyaye kamun kai.
Ta ce huɗubar Fadak da ta gabatar a Masallacin Annabi (S), neman haƙƙinta daga al’umma da hukumomin lokacin, ziyartar ƙaburburan shahidan Uhud da kuma amsa tambayoyi da shubuhohin aƙida da Fiƙihu, duk suna daga cikin misalan rawar da ta taka wajen jagorantar al’umma.
Dakta Ɗahira Da’awi ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan hanyoyin gina wayewar al’umma ita ce tsayawa tsayin daka wajen yaƙi da al’adun wulaƙanta mace. Ta ce hakan ya haɗa da tsoffin al’adun da suke kallon mace a matsayin marar cikakken matsayi, da kuma wasu tunanin zamani da suke mayar da ita kayan kasuwanci ko abin amfani kawai.
Ta ce Sayyida Fatima (SA) ta yi gwagwarmaya wajen kare mutuncin ɗan Adam daga waɗannan tunane-tunane guda biyu. A lokacin jahiliyyar Larabawa da ake binne ’ya’ya mata da rai, kuma ba a ba wa mace matsayi na mutunci, Allah Ya ɗaukaka Sayyida Fatima (SA) ta hanyar tarbiyyar Annabi (S), har ta kai matsayin shugabar matan talikai.
Ta ƙara da cewa ta gabatar wa duniya da sahihin matsayi da ma’anar mace ta hanyar ilimi mai amfani, kamun kai da neman haƙƙi bisa imani. Ta bayyana huɗubar Fadak a matsayin babban misali na wannan fafutuka, domin ta yi amfani da hujjoji, ilimi, jarumtaka da kyawawan ɗabi’u, ba hayaniya ko tayar da hankali ba.
Daidaito a fannoni daban-daban na rayuwar Sayyida Fatima (AS)
Da take magana kan ɓangaren ilimi na rayuwar Sayyida Fatima (AS), Da’awi ta ce koyarwar Alƙur’ani ta karya tunanin cewa dole ne mace ta zaɓi abu ɗaya ta bar wani. Ta ce mace ba lallai ne ta zaɓi tsakanin imani da ilimi, uwa da ci gaban kanta, kamun kai da shiga cikin al’umma, ko zaman lafiyar gida da neman adalci ba.
Ta bayyana yadda Sayyida Fatima (AS) ta tabbatar da wannan daidaito a rayuwarta:
- Imani da ilimi: Sayyida Fatima (AS) masaniya ce, kuma huɗubar Fadak tana ƙunshe da ilimomin Alƙur’ani, tauhidi, haƙƙoƙi da fikihu. A lokaci guda kuma, ta shahara wajen ibada da bautar Allah.
- Uwa da ci gaban kai: Ita ce mahaifiyar Imam Hassan da Imam Husaini (AS), Sayyida Zainab (AS) da Sayyida Kulthum (AS). Ta ba su tarbiyya mai kyau, amma hakan bai hana ta kasancewa mai ilimi, fahimta da taka rawar gani a cikin al’umma ba.
- Kiyaye kamun kai da shiga cikin al’umma: Ta kasance tana shiga cikin al’umma tare da kiyaye mutuncinta da kamun kai, tana kuma neman haƙƙinta. Wannan ya nuna cewa kamun kai ba ya hana mace taka rawar da ya kamata a cikin al’umma.
- Zaman lafiyar gida da neman adalci: A cikin gidanta ta kasance mata ta gari kuma uwa mai tausayi, yayin da a cikin al’umma ta kasance mai fafutukar tabbatar da adalci.
Mace a matsayin ginshiƙin sauya tarihin al’umma
Dakta Da’awi ta bayyana cewa tasirin mace a tsarin wayewar Musulunci bai tsaya ga wani zamani ko wani yanki ba, domin gudummawarta tana iya shafar tarihin al’umma da makomar bil’adama.
Ta ce a tsarin wayewar Musulunci, mace tana daga cikin muhimman abubuwan da ke motsa tarihin al’umma. Duk wani mataki da ta ɗauka wajen tarbiyya mai kyau, yaɗa ilimi da gyaran al’adu yana taimakawa wajen tsara makomar bil’adama.
Dangane da matsayin uwa a cikin tarbiyya, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka fi ɗorewa a tarihin Sayyida Fatima (AS) shi ne tarbiyyar zuriya masu gina wayewar al’umma.
Ta ce gidanta ya zama makarantar tarbiyyar Imamai da kuma abin koyi ga bil’adama. Haka kuma, ta ba Sayyida Zainab (AS) tarbiyyar da ta taimaka mata wajen taka muhimmiyar rawa a Karbala, Kufa da Sham, inda ta zama mai kiyaye tarihin al’umma da kyawawan ɗabi’u, tare da bambance koyarwar Allah daga tsoffin al’adu masu cike da camfi da wulaƙanci.
Ta ƙara da cewa akwai wasu muhimman fannoni na gudummawar Sayyida Fatima (AS), waɗanda suka haɗa da:
1. Isar da al’adu cikin basira: Ta kafa kyakkyawan misali na matsayin mace bisa mutuncin ɗan Adam, ba tare da nuna bambancin jinsi ba, tare da kiyaye ƙimomin Allah.
2. Samar da ilimi da warware manyan matsaloli: Amsar tambayoyin aƙida da Fiƙihu, da kuma bayanan ilimi da haƙƙoƙin da ke cikin huɗubar Fadak, tare da bayyana tushen Imamai da Wilaya, duk suna daga cikin gudummawarta wajen gina ilimi.
Yaƙin wayar da kai (Jihadut-Tabyin) a rayuwar Sayyida Fatima (AS)
Da take magana kan rawar Sayyida Fatima (AS) wajen bayyana gaskiya a cikin al’umma, Da’awi ta ce rawar da ta taka wajen isar da saƙo ba ta tsaya ga huɗubar Fadak kaɗai ba. A maimakon haka, ta yi amfani da hanyoyi daban-daban na isar da saƙo da wayar da kan al’umma.
Ta bayyana manyan hanyoyin da ta bi kamar haka:
1. Huɗubar Fadak a matsayin hanyar isar da saƙo ta magana da hujjojin haƙƙi
Dakta Da’awi ta ce huɗubar Fadak babban misali ne na isar da saƙo ta hanyar magana, inda Sayyida Fatima (AS) ta yi amfani da Alƙur’ani da Sunnar Annabi (S) wajen neman haƙƙi. Ta guji yaɗa jita-jita da cin mutuncin wasu. huɗubar ta ƙunshi fata, tunani mai zurfi da koyarwa, tare da bayyana halin da marasa galihu suke ciki.
2. Ziyartar ƙaburburan shahidan Uhud a matsayin saƙo ta hanyar aiki
Ta ce Sayyida Fatima (AS) tana yawan ziyartar ƙaburburan shahidan Uhud. Wannan ziyara ta kasance wata hanya ta isar da saƙo ba tare da magana ba, domin tana tunatar da al’umma muhimmancin sadaukarwa da shahada, da kuma kasancewa da aminci ga manufofin Annabi (S).
Haka kuma, wannan aiki ya kasance wata hanya ta nuna rashin amincewa da sauye-sauyen da suka fara bayyana a cikin al’umma, tare da raya tarihin Musulunci da ilmantar da sababbin tsararraki game da ƙimomin addini da matsayin Imamin al’umma.
3. Amsa tambayoyi da shubuhohi a matsayin hanyar yaɗa ilimin addini
Mai fafutukar yaɗa saƙonni ta kafafen sadarwa ta bayyana cewa Sayyida Fatima (AS) tana amsa tambayoyi da shubuhohin da ake gabatar mata a zamaninta. Wannan ya kasance wata hanya ta koyar da ilimin addini da bayyana gaskiyar aƙida.
Ta ce matan Madina da Sahabbai suna gabatar mata da tambayoyinsu, ita kuma tana amsa musu da hujjoji daga Alƙur’ani da Sunnar Annabi (S). Wannan ya taimaka wajen samar da ilimi da ƙarfafa fahimtar addini a cikin al’umma.
4. Ziyartar gidajen Muhajirai da Ansar da daddare bayan Saƙifa a matsayin fafutukar wayar da kai
Dakta Da’awi ta bayyana cewa ziyartar gidajen Muhajirai da Ansar da daddare bayan abin da ya faru a Saƙifa, duk da raunin da jikinta yake ciki, na daga cikin manyan hanyoyin da Sayyida Fatima (AS) ta yi amfani da su wajen bayyana gaskiya.
Ta bayyana cewa wannan mataki yana da fannoni huɗu:
- Fannin nuna rashin amincewa: Ta hanyar ziyartar gidajen Sahabbai da tattaunawa da su kai tsaye, tana tunatar da su abin da ya faru tare da bayyana musu hujjoji.
- Wayar da kan al’umma: Ziyarce-ziyarcen sun samar da hanyar sadarwa da tattaunawa wadda za ta taimaka wajen wayar da kan jama’a game da abin da ya faru.
- Tunatar da wasiyyar Annabi (S): Ta riƙa tunatar da mutane wasiyyoyin Manzon Allah (S), tare da bayyana matsayin Imam Ali (AS) da haƙƙinsa na jagoranci.
-Gwagwarmaya duk da raunin jiki: Fitowarta duk da raunin da take ciki ya kasance wata alama ta nuna irin zaluncin da aka yi mata, tare da ƙoƙarin wayar da hankulan al’umma domin su fahimci gaskiya.
A ƙarshe, Da’awi ta bayyana cewa Sayyida Fatima Zahra (AS) cikakkiyar abin koyi ce ga mata, domin ta haɗa imani, ilimi, kamun kai, tarbiyyar ’ya’ya, shiga cikin al’umma da fafutukar tabbatar da adalci.
Ta ce ta hanyar hanyoyi daban-daban na yaƙin wayar da kai, Sayyida Fatima (AS) ta nuna cewa yaɗa saƙo a Musulunci ba kawai amfani da kafafen sadarwa ba ne, illa dai wani nauyi ne na addini da ke taimakawa wajen gina tunani da asalin al’umma.
Ta ƙara da cewa Sayyida Fatima (AS) ta taka muhimmiyar rawa wajen gina wayewar al’umma, har ma abokan adawarta suka fahimci cewa ci gaba da wannan matsaya tata zai zama ƙalubale ga karkatattun manufofinsu. Saboda haka, ta kasance abin koyi ga dukkan mata da maza da suke son tafiya a kan tafarkin rayuwa mai tsarki da gina wayewar Allah.
Ra'ayinka